ABINDA YA KAMATA KUSANI DANGANE DA SECURITY DA EMERGENCYn WAYARKU.

Wayarka sirrinka, sannan kuma tana iya zamowa kariya a gareka!

Mutane da dama, ko kuma ince kusan kowa na amfani da kalmomin sirri (password) ko jage (pattern) domin tabbatar da tsaro akan wayoyin salularsu. Amma sai dai sau da dama hakan ka iya zamowa karan tsaye, a lokacin da mai wayar ke buƙatar agaji ko taimakon gaggawa a lokutan hatsari, rashin lafiya, ko ma mutuwa.

Amma da wannan taƙaitaccen ilimin da zan sanar da ku, wataƙila kuna iya taimakawa wani ko wata wajen tsirar da rayuwarsu ko lafiyarsu.

Mataki na ɗaya;

Idan wayarka na kulle za ta nuna “enter password”, a ƙarƙashin rubutun, zaka ga “emergency”. Ka danna emergency ɗin, zaka ga ” emergency information”. Sai ka danna ” emergency information” ɗin sau biyu, zaka ga alamar ” pencil ” ta fito a gefen dama, sai ka danna alamar “pencil ” ɗin domin shigar da rubutu.

Mataki na biyu;

A dai dai wannan gaɓar, kana iya shigar da lambobin wayar da kake son su zamo lambobin agajin gaggawa a gareka, watau “emargency contacts”

Kana iya shigar da lambobi da dama, amma ka tabbatar da cewa duk lambar da ka shigar, mai lambar na kusa da kai ne sosai. (ɗan uwa ko aboki).

Ka sani cewa duk lambar da ka shigar, ana iya kiranta ko da wayarka na kulle ba tare da an shigar da kalmar sirrinka ba (password).

Ta yadda za’a kira lambar da aka shigar a “emergency contacts”

Ka danna “emergency call” duk lambobin da aka shigar a matsayin “emergency contacts” zasu fito

Kana iya kiran lambobin ko baka bude wayar ba.

Allah yasa mu dace. Ameen

Leave a Comment