Yawancin ƴan Najeriya sunyi imanin cewa wanda suka sa a matsayin “next of kin” shine wanda zai ci gajiyar kuɗin dake cikin asusun bankinsu kai tsaye da zaran sun rasu. To amma gaskiyar maganar itace, idan “next of kin” ɗinka baida cikakken izini dangane da asusun bankinka kuma bakayi wata rubutacciyar wasiyya ba da zai halatta mashi cirar kuɗi daga assun bankinka ba bayan rasuwar ka, to ba zai samu cikakkiyar damar cirar kudi daga bankinka ba. A wannan gabar bankinka basu da abinda ya rage illa su bi wata hanyar da ake kira “LEGAL PROBATE” a turance.
LEGAL PROBATE na nufin wata hanyar tantance asalin wanda zai gaji kuɗin dake asusun mamaci watau “next of kin”. Wannan hanyar na da matukar wahala da kuma kashin kuɗi. Ko da anyi nasara wajan tantance magaji a wannan hanyar, to dole sai magaji ko magada sunyi hasarar wani kaso mai tsoka daga cikin kuɗin da suka gada a wajan harkar zirga-zirgar kotu da sauran wasu sharuɗɗa da doka ta tanada.
Domin kaucewa waɗanan matsalolin, kawai kaje bankinka ka nemi a baka abinda ake kira “POD FORM”. POD na nufin “PAYBLE ON DEATH” (biyan kuɗin mamaci bayan mutuwa). Sai ka rubuta suna ko sunayen mutanen da kake son a ba kuɗinka bayan ka bar duniya a cikin POD FORM ɗin. Abinda kawai magajin ka zai kai a banki shine takardar shedun mutuwarka, shike nan sai abashi dukkan abinda ke cikin asusun a sauƙake.
Da POD FORM, iyalanka ba za su shiga wata matsalar zirga-zirgar kotu ba ko shige da ficen da ka iya jawo hasarar wani kaso mai tsoka daga cikin kuɗaɗen da ka barma su ba. Allah yasa mu cika da imani. Ameen.
Kada mu manta, mu tura wannan rubutu zuwa ga ƴan uwanmu da abokan arziki domin faɗakar da su da sauran al-umma.
Yana da kyau ku karanci Matsayar CBN Akan Dakatar da OPAY da PALMPAY
ABINDA YA KAMATA KUSANI DANGANE DA SECURITY DA EMERGENCYn WAYARKU.