Matsayar CBN Akan Dakatar da OPAY da PALMPAY

Matsayar CBN Akan Dakatar da OPAY da PALMPAY

Babban bankin bankuna na Najeriya watau CBN ya bayyana Matsayar sa akan labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da bakunan mutane da ke cewar za’a rufe ƙana nan bankunan yanar gizo (Fintech companies) kamar su OPAY da PALMPAY.

Babban bankin, yayi watse da maganar ya kuma ce wannan labarin ƙanzon kurege ne wanda bashi da tushe.

Kampanin ruwaito labarai na Najeriya watau ‘News Agency of Nigeria’ (NAN), ya ruwaito daraktan riƙon ƙwarya a ɓangaren yaɗa labarai na CBN Mr. Isah Abdulmumin a ranar jum’a 24 ga watan Maris, 2023 na cewa, labarin dakatar da kampanonan ba gaskiya bane.

Wane Labari ne Ake Yaɗawa?

Labarin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta dangane da wadannan kampanonan yazo ta harshen turanci kamar haka; “Please if you are using OPAY, PALMPAY or any of these CHINA APPs or their POS, stop keeping much money in the account or stop using it.The CBN is about suspending their accounts because these apps are being used to perpetrate fraud.’’

Fassara; ” Don Allah idan kana amfani da OPAY, PALMPAY, da duk wani kalar manhajar China ko POS ɗinsu, ka daina aji kuɗi mai yawa acikinsu ko ka daina amfani dasu gaba ɗaya. CBN tana gab da rufe manhajojin su, sabo da ana amfani dasu wajan aikata laifuka da almundahana a ɓangaren kuɗi”

KU KARANTA: PUBLIC GUIDE TO PHONE SECURITY AND EMERGENCY EVERYONE MUST CARE TO KNOW

Mey OPAY da PALMPAY Suka ce?

Su ma kampanonan da aka yaɗa jita-jitar akansu sun mayar da martani a lokuta daban-daban ta shafukan sada zumunta, inda suka ƙaryata labarin.

OPAY

OPAY sun mayar da martani a shafukansu na sada zumunta kamar haka ““the post mentioning the CBN shutting down our operations is false and misleading to the general public.’’

Fassara; Maganar dake yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa CBN zai rufe kampaninmu ba gaskiya bane, anyishi ne domin batarwa da tada hankulan jama’a”.

Palmpay

Suma dai PALMPAY ba’a barsu a baya ba wajan maida martanin. PALMPAY sun yi nasu martanin kamar haka ““We are aware of news currently being spread on social media about CBN shutting down the operations of PALMPAY.

Fassara; muna sane da labaran ƙaryar da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta dake cewa CBN zai dakatar da hada hadarmu.

2 thoughts on “Matsayar CBN Akan Dakatar da OPAY da PALMPAY”

Leave a Comment